Komishinonin Ayyukan Gona na Nigeria bakidaya sun gabatar da zama na musamman A Garin Jos Dake Jahar Plateau.....
A safiyar yaune Komishinan Ayyukan Gona na Jahar Gombe Honourable Muhammad Magaji Gettado ya samu damar halartan taron Komishinonin ayyukan gona na Jahohi 36 dake tarayyar Nigeria domin gabar da zama kamar yadda sukeyi kowane shekara akan abun da ya shafi cigaban harkokin noma da kiwo a Nigeria.
Taron wanda aka sabayi kowane shekara an fara tun ranar litin za'a gama shi ranar Jumma'a mai zuwa wanda Minsitan Ayyukan Gona da raya karkara na kasa Hon Muhammad Mamud Abubakar yake jagoran ta ya samu halartan Komishinonin Ayyukan Gona na Jahohin Nigeria 36 tareda sakatarorin ma'aikatun dakuma Directors tareda muhimman mutane masana yananyi dakuma ayyukan gona.
Masana da yawa sun halarci wannan taron domin haduwa gabadaya don su duba matsaya da aka cimma daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu don su duba yanayin ayyukan gona a Jahohin Nigeria bakidaya sannan kuma a sake daukan matsaya na ayyukan da za'ayi domin raya ayyukan dabbobi, karkara dakuma daukacin ayyukan gona na shekara mai zuwa.
Taron wanda aka saba haduwa kowane shekara domin duba hanyoyi da za'a fitar wajen ganin cewa an fidda sabbin tsare tsare wanda zai kawo cigaba a ayyukan gona wanda ake sa ran zuwa karshen zaman kowacce Jaha zata gabatar da nata bukatun domin zaman tq amice dasu wajen sanya su a budget na sabuwar shekarar mai zuwa.
Daga karshe sun kai ziyaran aiki a gonan kifi mai girma a garin Jos domin ganewa idon su yadda yanayin kiwo kifin yake tafiya domin karawa juna sani dakuma bada shawarwarin da ya kamata.
Muna fatan yadda aka fara wannan taron lafiya Allah yasa agama lafiya.
Bashir Sulaiman Garkuwa
Personal Assistant to Hon. Com of Agriculture and Animal Husbandry
Gombe State
14/9/2022
Post a Comment